Isa ga babban shafi
Sahel

Alqa'ida ta yi umarnin kai wa kamfanonin kasashen yamma a Sahel hari

Aqmi, wanda shi ne reshen kungiyar Alqaida a Yankin Sahel da Magreb, ya bukaci magoya bayansa da su kai hari akan kaddarorin kasashen yammacin duniya da ke shimfide cikin yankin na Sahel.

Jagoran Alga'eeda a Aljeriya Abou Moussa Abdelouadoud.
Jagoran Alga'eeda a Aljeriya Abou Moussa Abdelouadoud. AFP PHOTO/HO
Talla

A sanarwar da ta fitar a yammacin jiya talata, Kungiyar ta Aqmi ta bukaci kamfanoni da masana’antu mallakin kasashen na yammacin duniya da su gaggauta dakatar da ayyukansu a cikin kasashen na Sahel, domin kuwa tuni ta umurci baradenta da su kaddamar da hre-hare a kansu.

Sanarwar ta ce wannan gargadi ne da ya shafi illahirin kasashen yankin na Sahel da suka hada da Mauritania, Mali, Senegal, Burkina Faso, Nijar da kuma Chad.

Kungiyar ta ce bai kamata a dauki wannan gargadi da wasa ba, domin umarni ne da ya fito daga jagoran Alqa’ida Ayman Al-zawahiri, kuma ko baya ga kasashen Sahel, za a iya fadada hare-haren har zuwa kasar Libya.

Aqmi dai kungiya ce da ta share tsawon shekaru tana kai hare-hare tare da yin garkuwa da mutane cikin na yankin Sahel, dalilin da ya sa masana harkar tsaro irinsu Wassim Nasr, da ke zaune a Faransa ke cewa ya kamata a dauki gargadin da muhimmanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.