Isa ga babban shafi
Libya

IS ta dauki alhakin kaddamar da hari a Libya

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kaddamar a babban ofishin hukumar zaben kasar Libya da ke birnin Tripoli da tsakar ranar yau Laraba wanda ya hallaka fiye da mutane 12 baya ga jikkata wasu da dama.Ma'aikatar lafiyar kasar ta tabbatar da mutuwar mutanen 12 yayinda ta ce adadin ka iya karuwa la'akari da yawan wadanda suka jikkata.

Libya dai na fama da matsalar tsaro ne tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi a shekarar 2011 wanda ya yi mulki tsawon shekaru 42 kuma ya haramta yin zabe.
Libya dai na fama da matsalar tsaro ne tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi a shekarar 2011 wanda ya yi mulki tsawon shekaru 42 kuma ya haramta yin zabe. REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce tun farko wasu mutane hudu ne suka tunkaro ginin Ofishin hukumar ta zabe da ke tsakiyar birnin na Tripoli inda biyu suka ta shi bom din da ke jikinsu yayinda sauran biyun kuma suka bude wuta kan jama'ar da ke gurin.

Shaidun gani da ido sun ce bayan kaddamar da harin babu abin da su ke gani face hayaki da ya turnuke sararin samaniya sai kuma karar musayar bindugu tsakanin mayakan na IS da kuma jami'an tsaro.

Tuni dai gwamnatin hadin kan kasar ta GNA ta tabbatar da harin tare da yin tir da shi yayinda  abangare guda itama Majalisar dinkin duniya ta yi tir da harin tare da aike sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Gwamnatin hadin kan kasar dai a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce makamantan hare-haren baza su dankwafar da kasar kamar yadda mayakan ke tsammani ba.

Libya dai na fama da matsalar tsaro ne tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi a shekarar 2011 wanda ya yi mulki tsawon shekaru 42 kuma ya haramta yin zabe.

Sai dai bayan hambarar da gwamnatinsa ne a shekarar 2012 da kuma 2014 amma duk da haka kasar ke fama da babbar barazana.

A shekarra 2015 ne kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kafa gwamnatin hadin kan kasa amma kawo yanzu ake ci gaba da fuskantar mabanbantan matsaloli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.