Isa ga babban shafi
Chad

Amurka ta bai wa Chadi jirage don yaki da ta'addanci

Amurka ta bai wa Chadi kyautar wasu kananan jiragen sama guda biyu domin amfani da su wajen yaki da ta’addanci. An mika jiragen biyu ne a wajen wani bikin da aka gudanar a sansanin sojin sama da ke N’Djamena.

Amurka ta kuma taimaka wajen gina inda ake aje jiragen da kuma wurin gyaran su a Chadi, bayan da ruwan sama da guguwa suka lalata sansanin sojin saman kasar.
Amurka ta kuma taimaka wajen gina inda ake aje jiragen da kuma wurin gyaran su a Chadi, bayan da ruwan sama da guguwa suka lalata sansanin sojin saman kasar. AFP
Talla

An mika wadanan jiragen guda biyu masu inji guda guda da ake kira ‘Cessna 208Bs’ ne a wajen wani biki da aka gudanar a sansanin sojin saman Chadi da ke birnin Ndjamena.

Tun a karshen shekarar da ta gabata aka kai jiragen Chadi inda ake amfani da su wajen koyar da matuka jirage.

Amurka ta kuma taimaka wajen gina inda ake aje jiragen da kuma wurin gyaran su a Chadi, bayan da ruwan sama da guguwa suka lalata sansanin sojin saman kasar.

Jakadan Amurka a Chadi, Geeta Pasi ya ce sun kashe kudin da ya kai Dala miliyan 43 wajen aikin, yayin da ya bayyana Chadi a matsayin kawar Amurka wajen yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.