Isa ga babban shafi
Burundi

An kaddamar da yakin neman zaben raba gardamar Burundi

An Kaddamar da yakin neman zaben raba gardamar kasar Burundi wanda zai bada damar amincewa da sauye sauyen da aka yiwa kundin tsarin mulkin da zai baiwa shugaba Pierre Nkurunziza damar cigaba da zama a karagar mulki.

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi.
Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi. AFP PHOTO / MARCO LONGARI
Talla

Jam’iyyu 26 da ke alaka da Jam’iyya mai mulki aka baiwa damar gudanar da yakin neman zaben da za’ayi ranar 17 ga wata.

Jam’iyyun adawar kasar sun yi kira ga magoya bayan su da su kauracewa zaben.

Yarjejeniyar da aka kulla ta Arusha a shekarar 2000 ta ce babu shugaban da zai wuce wa’adi biyu na shekaru 10, abin da shugaba Nkurunziza ya sa kafa ya shure wajen sauya kundin tsarin mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.