Isa ga babban shafi
Nijar

Barazanar Hukumomin Nijar na rufe gidajen abincin dalibai na kasar

Gwamantin Jamhuriyar Nijar tayi barazanar rufe daukacin shagunan sayar da kaya da kuma gidajen sayar da abinci dake cikin jami’oin kasar daga gobe litinin, muddin ba’a kawo karshen rikicin da ake samu a Jami’ar Yammai ba.

Zanga-zangar daliban jami'ar Yammai dake Nijar
Zanga-zangar daliban jami'ar Yammai dake Nijar BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Kakakin gwamnatin kasar Assoumana Malam Isa yace gwamnati ta damu da yadda dalibai ke kauracewa azuzuwa yayin da harkokin bada ilimi suka kankama.

Gwamnatin ta bukaci daliban da su koma cikin azuzuwan su domin karbar darasi daga gobe litinin ko kuma ta dauki matakan da suka dace.

Jamhuriyar Nijar na da jami’oi guda 8 dake dauke da dalibai 37,000, yayin da jami’ar Yammai ke da dalibai 23,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.