Jahilci ne ya haddasa rikicin Makiyaya da Manoma - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce idan da bai yi karatu ba shima da ya kasance cikin rikicin Makiyaya da Manoma da ya addabi kasar tare da gurgunta al'amuran tsaro a wasu yankunan.
Wallafawa ranar:
Muhammadu Buhari wanda ke sanar da hakan yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriyar ya kuma bukaci iyaye da su jajirce wajen ganin sun sanya yaransu a makarantu.
A cewarsa galibin rikice-rikicen na faruwa ne sanadiyyar rashin ilimi daga bangarorin biyu masu fada da juna.
Ziyarar shugaba Buharin zuwa Bauchi ita ce ta farko tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015 inda ya kaddamar da wasu tarin ayyuka da suka kunshi asibiti, tituna da kuma wasu kayakin noma ga al'ummar jihar.
Kafin yanzu dai, Muhammadu Buhari a lokuta da dama ya shirya zuwa Bauchin amma yana soke tafiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu