Isa ga babban shafi
Kamaru-Najeriya

Kamaru na tiso keyar yan gudun hijarar Najeriya zuwa gida

Hukumar Majalisar dinkin Duniya dake kula da yan gudun hijira ta bayyana matukar damuwa a kan yadda kasar Kamaru ke ci gaba da tiso keyar yan gudun hijrar Najeriya zuwa gida.

Flippo Grandi, shugaban hukumar yan gudun hijira dake aiki da MDD
Flippo Grandi, shugaban hukumar yan gudun hijira dake aiki da MDD TONY KARUMBA / AFP
Talla

Yan Najeriya 385 ne kasar ta Kamaru ta tilastawa ficewa daga kasar daga farkon Shekarar nan zuwa wannan lokaci.

Ranar 10 ga watan Afrilu na wannan shekara hukumar yan gudun hijira ta tattance mutane 160 yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya tilasatawa baro gidajen su aka mayar da su gida Najeriya.

Yayinda a karshen wannan watan mutane 87.600 ne hukumar ta samu yi masu rijista a matsayin yan gudun hijira a Kamaru.

Hukumomin Kamaru sun musanta zargin da hukumar ta yi a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.