Isa ga babban shafi
Swaziland

Kasar Swaziland ta canza suna

Sarki Mswati na uku na kasar Swaziland ya sauya sunan kasar sa zuwa ESwatini a lokacin da ake bukin cikan kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai daga kasar Birtaniya.

Sarki Mswati III na kasar Eswatini tsohuwar Swaziland
Sarki Mswati III na kasar Eswatini tsohuwar Swaziland Wikimedia
Talla

Ba kamar sauran kasashe ba, ita kasar Swaziland bata sauya sunan kasar ba a lokacin da ta samin mulkin kai a shekara ta 1968 bayan data kwashe shekaru samada 60 karkashin ikon Birtaniya.

Sarkin kasar Mswati na 3, wanda yake jawabi a filin wasanni dake Manzini babban gari na biyu cikin kasar , kuma cikin kayan soja jajaye, ya fadi cewa lokaci yayi da kasar za ta amsa sunan ta na usuli.

Yace kasashen Africa a lokacin samun ‘yancin kai sukan maida sunayensu na usuli ne kafin mulkin mallakan, saboda haka ne daga yanzu sun goge sunan Swaziland za’a rika kiran kasar Eswatini.

Yace kalmare Swaziland kan rika bata ran wasu ‘yan kasar domin an gama ne da harshen turanci da Swazi.

Sarkin yace sun dauki shekaru suna nazarin wannan sauyi, domin majalisar kasar ta dauko batun a shekara ta 2015.

Shi dai wannan Sarki wanda aka nadawa Sarautar a shekara ta 1986 a lokacin da yake da shekaru 18, na shan suka wajen wasu mutan kasar saboda son fachaka da dukiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.