Isa ga babban shafi
Chadi

Fararen hula na son Majalisar Chadi ta yi watsi da sabon kundin mulki

Kungiyoyin fararen hula a Chadi, sun bukaci Majalisar dokokin kasar da ka da ta amince da Daftarin Sabon Kundin tsarin mulkin da aka gabatar ma ta.Kungiyoyin sun ce da farko ‘yan majalisar ba sa da halaccin jama’ar kasar tun 2015, sannan kuma sauye-sauyen da ke kunshe a kundin tsarin mulkin sun yi hannun riga da abinda ake kira dimokuradiyya.

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby.
Shugaban Kasar Chadi Idris Deby. REUTERS/Alain Jocard/Pool
Talla

A baya-bayan nan ne dai Gwamnatin Chadi bayan wasu jerin taruka ta sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasar da yanzu haka sahalewar Majalisar kadai ya ke bukata.

Tun farko dai sauya fasalta kundin tsarin mulkin ya biyo bayan kiraye-kirayen hakan daga al'ummar kasar a cewar ta hakan ne za a kawo karshen takaddamar siyasar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.