Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zimbabwe ta kori ma'aikatan jinya dubu 4 daga bakin aiki

Gwamnatin Zimbabwe ta kori dukkanin kananan likitoci da suka shiga yajin aiki domin neman kara masu albashi. Adadin wadanda aka kora daga aikin zai kai mutane dubu 4 kamar dai yadda mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga, ya sanar.

Gwamnatin ta Zimbabwe dai na zargin ma'aikatan jinyar da fakewa da aikinsu wajen nuna adawar siyasa gareta duk da matakan inganta bangaren lafiyan da ta ke dauka.
Gwamnatin ta Zimbabwe dai na zargin ma'aikatan jinyar da fakewa da aikinsu wajen nuna adawar siyasa gareta duk da matakan inganta bangaren lafiyan da ta ke dauka. REUTERS/Philimon Bulaway
Talla

Tuni dai aka kwashe dubban marasa lafiyan da ke kwance a mabanbanta asibitoci tare da raba su zuwa manyan asibitocin kasar kafin daukar mataki na gaba.

Dubban jami'an kiwon lafiyar dai na bukatar gwamnatin kasar ta kara musu albashi tare da alawus-alawus duk kuwa da cewa a baya gwamnatin ta fitar akalla dalar Amurka miliyan 17 don habaka bangaren lafiyar kasar.

Kalaman mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga ya zargi jami'an da fakewa da aikinsu wajen nuna adawar siyasa ga gwamnati mai ci.

Chiwenga ya ce gwamnati za ta yi hayar tsaffin jami'an kiwon lafiyar don ci gaba da jan ragamar harkokin lafiyar kafin daukar mataki na gaba.

Sanarwar da kungiyar jami'an kiwon lafiyar ta fitar a yau ta ce sun samu sanarwar mataimakin shugaban kasar kuma hakan ba zai hana su ci gaba da yajin aikin don neman hakkokinsu ba.

Kungiyar dai ta koma yajin aikin ne bayan wanda ta shafe mako guda tana yi a cikin watan nan kan abin da ta kira rashin biya mata wasu hakkokinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.