Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Malam Nuhu Abdu Magaji kan arangamar kungiyoyin fararen hula da jami'an tsaro kan dokar haraji a Nijar

Wallafawa ranar:

A jiya lahadi an yi wata taho mugama tsakanin yan sanda da masu zanga zangar tsadar haraji wanda majalisar dokokin Nijar ta amince da ita a dokar kasafin kudin kasar na bana da suka yi biris da hanin da mahukunta suka yi masu kan zanga zangar.Taho mu gamar ta jiya dai, ta bada damar kama halifofin da suka maye gurbin shugabanin kungiyoyin farar hular da aka kama kuma aka tura kurkuku makwanni uku da suka gabata, sakamakon suma biris da hanin na gwamnati kan zanga zangar. To domin jin yadda wasu masharhanta halin da ake ciki a kasar ta Niger ke kallon wannan badakala da kuma yanhohin magance ta, Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Malam Nuhu Abdu Magaji daga birnin Konni da ke cikin yankin Tawa ga kuma yadda firar ta kasance.

Wasu jami'an tsaron Nijar lokacin da su ke tisa keyar shugabannin kungiyoyin fararen hular da suka ki amsa umarnin gwamnati na dakatar da zanga-zanga.
Wasu jami'an tsaron Nijar lokacin da su ke tisa keyar shugabannin kungiyoyin fararen hular da suka ki amsa umarnin gwamnati na dakatar da zanga-zanga. Moussa Kaka/RFI
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.