Isa ga babban shafi
Mali

An kai wa Dakarun MDD hari a Mali

Akalla sojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin Duniya 6 ne suka jikkata a wani harin bazata da aka kai musu a yankin Arewacin kasar Mali.

Yan tawayen Tombouctou na kasar Mali
Yan tawayen Tombouctou na kasar Mali AFP PHOTO / AFPTV / FRANCE 2
Talla

A sakon twitter da ta fitar a yau asabar majalisar ta tabbatar da cewar an kai kazamin harin a sansaninta na Timbuktu da ke Arewacin kasar Mali, inda aka samu musayar wuta da kuma kunar bakin wake ta hanyar anfani da Mota.

Sanarwar ba ta yi karin bayani kan rasa rayuka ba, sai dai cewa al’amurra sun lafa ya zuwa yanzu.

Majalisar Dinkin Duniya na da sojoji dubu goma sha uku 13,000 da ‘yan sanda a kasar ta Mali, in da yawancin su na a Arewacin kasar ne.

A wannan shekara kadai sojojin kiyaye zaman lafiya 7 da ke a bakin aikinsu ne aka hallaka, a harin da aka baiyana a matsayin mafi muni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.