Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka mutane 41 a Taraba da Benue cikin dare

Rahotanni daga Jihohin Taraba da Benue sun ce wasu Yan bindiga sun kai kazamin hari daren jiya, inda suka hallaka mutane 41, yayinda wasu da dama suka bata.

Ko a jiya Laraba ma Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya dora laifin yawaitar mahara masu fakewa da sunan Fulani Makiyaya da kuma sauran 'yan bindiga kan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Ghaddafi, inda ya ce tun farko shi ne ya damka musu makamai.
Ko a jiya Laraba ma Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya dora laifin yawaitar mahara masu fakewa da sunan Fulani Makiyaya da kuma sauran 'yan bindiga kan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Ghaddafi, inda ya ce tun farko shi ne ya damka musu makamai. Reuters
Talla

Harin na zuwa ne kwana guda bayan wani hari da aka ce wasu mutane sanya da kayan soji suka kai, wanda ya hallaka mutane 10.

Bayanai sun ce an kai harin ne a karamar hukumar Logo dake Jihar Benue da kuma Wukari dake Jihar Taraba.

Ya zuwa yanzu jami’an tsaro ba su yi karin haske kan harin ba.

Ko a jiya Laraba ma Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya dora laifin yawaitar mahara masu fakewa da sunan Fulani Makiyaya da kuma sauran 'yan bindiga kan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Ghaddafi, inda ya ce tun farko shi ne ya damka musu makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.