Isa ga babban shafi
Algeria

Gwamnatin Algeria ta ayyana zaman makoki

Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflikaya ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki bayan faduwar Jirgin saman Soji da ya yi sanadin mutuwar mutane 257 lokaci guda, akasarinsu sojoji da iyalansu.

Wurin da aka samu hatsarin jirgin saman sojin Algeria
Wurin da aka samu hatsarin jirgin saman sojin Algeria ENNAHAR TV/Handout/ via REUTERS
Talla

Baya ga zaman makokin da za a yi a dukkanin fadin kasar na kwanaki 3, shugaban kasar ya kuma bayyana cewar za a yi wa mamatan addu’a ta musamman a daukacin Masallatan kasar a gobe Jumu’a.

Ma’aikatar tsaron kasar ta Algeria ta tabbatar a cikin wani bayani da ta gabatarwa manema labarai cewar, fasinjoji 247 da ke  cikin jirgin da ma’aikatan jirgi 11 sun mutu ne ba tare da ko dayansu ya samu ceto ba.

Bayannai daga kasar ta Aljeria na cewar a baya-bayan nan kasar ta sha fama da hatsurran jiragen sama na jigila da kuma na soji domin ko a watan Disamban shekarar 2012, wasu jiragen sun yi taho-mu-gama a yankin Tlemcen lokacin da sojin ke koyon tuki.

A watan Fabairun 2014, wasu mutane 77 sun mutu lokacin da wani jirgin sojin ya fadi a tsakanin Tamanrasset da ke yankin kudancin Algeria da kuma gabashin birnin Costantine dauke da wasu jami’an sojin kasar da iyalansu .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.