Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Dubban jama'a na bore kan kisan fararen hula a Afrika ta tsakiya

Daruruwan Mutane ne suka gudanar zanga zanga domin nuna bacin ran su da kisan da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka yi wa mutane 17 a kusa da birnin Bangui da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Masu zanga zangar sun gabatar da gawarwakin mutanen da su ke zargin sojojin da kashewa a gaban sansanin na su.
Masu zanga zangar sun gabatar da gawarwakin mutanen da su ke zargin sojojin da kashewa a gaban sansanin na su. PHOTO | AFP
Talla

Masu zanga zangar sun gabatar da gawarwakin mutanen da su ke zargin sojojin da kashewa a gaban sansanin na su.

Wannan bore na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban aikin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Jean-Pierre Lacroix ke ziyara a kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniyar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar sun ce 'yan bindiga sun kashe sojin Rwanda guda, kana sun raunana wasu 8 a harin da aka kai musu jiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.