Isa ga babban shafi
Mali

'Yan bindiga sun hallaka magajin gari a Burkina Faso

Wasu ‘yan bindiga da ba a gane su ba, sun harbe Magajin Garin wani birni da ke Arewacin Burkina Faso, Hamidou Koundaba har lahira a kusa da iyakar Mali.

Hoton wasu daga cikin mayakan kungiyoyin jihadi a kasar Mali gab da iyakar Burkina Faso.
Hoton wasu daga cikin mayakan kungiyoyin jihadi a kasar Mali gab da iyakar Burkina Faso. AFP PHOTO / AFPTV / FRANCE 2
Talla

Majiyar jami’an tsaro ta ce ‘Yan bindigar akan babur sun bude wuta kan Magajin Garin ne kusa da gidan sa, kana kuma suka tsere.

Shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore yayi Allah wadai da kisan.

Burkina Faso dai na fama da hare-haren ba gaira babu dalili baya ga ayyukan ta’addanci da su ke kara ta’azzara da kuma hare-hare kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Ko a watan da ya gabata ma wasu tagwayen hare-haren ta'addanci da mayakan masu ikirarin jihadi suka kai gab da Ofishin jakadancin Faransa a babban birnin kasar ya hallaka mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.