Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Mahara sun bude wuta kan dakarun wanzar da zaman lafiya a Bangui

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kisan dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya inda ta ce wasu yan bindiga ne suka bude wuta kan sansanin dakarun na ta da ke birnin Bangui na kasar.

Kawo yanzu dai Majalisar ta ce bata kai ga gano wadanda suka kai harin ba, haka zalika ba ta bayyana adadin dakarun da suka kwanta dama ba.
Kawo yanzu dai Majalisar ta ce bata kai ga gano wadanda suka kai harin ba, haka zalika ba ta bayyana adadin dakarun da suka kwanta dama ba. (Photo : AFP)
Talla

Sanarwar da Majalisar ta bayar, ta nuna cewar an kai harin ne da misalin karfe 11 na dare a gidajen da dakarun kasashen Masar da Jordan ke zama, abinda ya haifar da musayar wuta tsakanin dakarun da Maharan.

Vladimir Monteiro, mai magana da yawun Majalisar ya ce ya zuwa yanzu basu kai ga gano wadanda suka kai harin ko kuma wadanda ke da hannun a kitsa shi ba.

Haka zalika Majalisar ba ta fayyace adadin Dakarun da suka kwanta dama ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.