Nijar ta aike da shugabannin fararen hula gidan Yari
Akalla shugabannin manyan kungiyoyin fararen hula 4 ne yanzu haka ke garkame a gidan yarin Jamhuriyar Nijar bayan zanga-zangar karshen mako don kin jinin dokar haraji da gwamnatin ta haramta wadda ta juye zuwa rikici.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugabannin hudu na daga cikin mutane 23 da jami'an tsaro suka kame tun ranar Lahadi bayan da suka fito zanga-zanga duk da hanin da gwamnati ta yi.
Daga cikin shugabannin fararen hular da gwamnatin ta kame akwai wani jagoran adawa Nouhou Arzika sai masu fafutukar kare hakkin dan adam Moussa Tchangari da Ali Idrissa da kuma Lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam Lirwana Abdourahamane.
Gwamnatin ta Nijar ta ce ta haramta zanga-zangar ta ranar Lahadi ne saboda an shiryata a kuraren lokaci, yayinda ta ce mutanen hudu ta na zarginsu da jagorantar lalata dukiyar al'umma da kuma karya dokar gwamnati.
Tun a jiya Litinin ne dai kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bukaci sakin mutanen 23 cikin gaggawa, amma maimakon hakan zai gwamnatin ta iza keyar shugabannin hudu zuwa gidan yari.
Tuni dai gwamnatin ta Nijar ta yi umarnin kulle gidan talabijin da na Rediyo mallakin Ali Idrissa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu