Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta tara kudin shiga fiye da Naira tiriliyan 8

Ministar Kudin Najeriya Mrs. Kemi Adeosun ta ce zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ta tara kudaden shiga da yawansu ya haura sama da Naira Tiriliyan 8, tun bayan da gwamnatin Najeriya ta fara amfani da asusun ajiya na bai daya wato TSA.

Ministar kudin Najeriya Mrs Kemi Adeosun.
Ministar kudin Najeriya Mrs Kemi Adeosun.
Talla

Kemi Adeosun wadda ke sanar da hakan a jawabin da ta gabatar gaban wani kwamitin majalisar wakilan kasar da ya nemi jin Karin bayani akan al’amuran tafiyar da tsarin asusun ajiyar bai dayan na gwamnatin Najeriya.

Adeosun ta bayyana cewa kafin fara amfani da asusun ajiyar na bai daya, Gwamnatin na tafka asarar sama da naira biliyan 70, kusan a duk shekara, ko kasa da haka, ta hanyar zurarewar kudaden ta hanyoyin da basu dace ba, daga ciki asusun ajiya daban daban har 17,000, wadanda ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnatin kasar ke amfani da su.

A baya-bayan nan ne dai hukumar kididdiga ta Najeriyar ta sanar da cewa tarin basukan da ake bin kasar na ciki dana waje a karshen shekarar 2017,  ya kai naira Triliyan 10.

Hukumar ta ce bashin ya hada da na cikin gida da kuma wanda gwamnatin ta karbo daga kassahen ketare, inda kididdiga ta nuna cewar bashin cikin gida da ke kan Najeriya ya kai kusan Naira Triliyan 7 yayin da kuma bashin da kasar ta karbo daga ketare ya kai naira Triliyan 3 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.