Chadi
Chadi ta amince da sauya fasalin tsarin mulkinta
Kasar Chadi ta amince da aiwatar da tsarin mulkin shugaban kasa da mataimakin sa kamar yadda majalisar sauyawa kasar fasalin tsarin mulki ta amince da shi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
A karkashin sabon tsarin da yan siyasa da kungiyoyin fararen hula suka amince da shi, za’a kirkiro ofishin mataimakin shugaban kasa da kuma wa’adin shekaru 6 na shugaban kasa da za’a maimaita sau guda.
Tsarin ya kuma amince da shekaru 5 na wa’adin Yan Majalisun kasar wanda za’ayi sau biyu kawai.
Yan adawa sun kauracewa taron.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu