Isa ga babban shafi
Masar

An fara kada kuri'u a zaben shugabancin Masar

An bude tashoshin kada kuri’u a Masar, in da ake gudanar da zaben shugaban kasa tsakanin shugaba Abdel Fatah al Sisi da wasu 'yan takaran da ba su yi fice ba a siyasar kasar.

Ana saran shugaba Abdel Fatah al Sisi zai lashe zaben
Ana saran shugaba Abdel Fatah al Sisi zai lashe zaben REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

An bude tashoshin ne da misalin karfe 7 agogon GMT, kuma za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da zaben wanda ake hasashen zai bai wa shugaba al Sisi wa’adi na biyu ba tare da matsala ba.

An tsaurara matakan tsaro sosai a fadin kasar saboda barazanar kungiyar da ke tada kayar baya wadda ta yi alkawarin kai hari a wuraren zaben.

Mutane sama da miliyan 60 suka yi rajistar kada kuri’ar, a zaben da ake saran samun sakamakonsa ranar 2 ga watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.