Isa ga babban shafi
Ghana

Amurka zata girke sojojinta a Ghana

Majalisar Ghana ta amince da bai wa Amurka damar girke sojojinta a kasar, kudurin da bai samu amincewar ‘yan adawa a zauren majalisar ba, wadanda suka kaurcewa kada kuri’a a kansa.

Sojojin Amurka yayin halartar wani atasaye a kasar Poland.
Sojojin Amurka yayin halartar wani atasaye a kasar Poland. REUTERS/Kacper Pempel
Talla

Kudurin ya bai wa Amurka damar shigo da dukkanin kayayyakin da suke bukata cikin kasar ba tare da biyan haraji ba, a karakshin yarjejeniyar, Amurka zata samar da akalla dala miliyan 20 domin wadata sojin Ghana da kayakn aiki tare da basu horo, inda zasu rika gudanar da tasasyen hadin gwiwa.

To sai dai masu adawa da shirin da suka hada da wasu kungiyoyin fafutuka, na kallo wannan yarjejeniya a matsayin kaskanci ga kimar da kasar ta Ghana ke da ita, a matsayin ‘yantacciya.

A ranar Juma’a da lamarin ya faru, wasu jerin gwanon masu zanga-zanga suka yi kokarin kutsawa harabar majalisar kasar don tilastawa ‘yan majalisar janye goyon bayan matakin, sai dai jami’an tsaro sun hana su damar aiwatar da aniyar ta su.

A ‘yan watannin baya Amurka ta karfafa ayyukan sojinta da ta girke a Jamhuriyar Nijar, domin yaki da ta’addanci, matakin da har yanzu wasu hankalinsu bai kwanta da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.