Isa ga babban shafi
Kamaru

An hallaka kwamishina a yankin 'yan awaren Kamaru

Wasu mahara da ake kyautata zaton sun fito daga yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru sun hallaka Kwamishinan Kula da Harkokin Filaye a kudu maso yammacin kasar.  

Wani gida da harin bama-bamai ya ritsa da shi a yankin da ke fama da tashin hankali a Kamaru.
Wani gida da harin bama-bamai ya ritsa da shi a yankin da ke fama da tashin hankali a Kamaru. REUTERS/Josiane Chemou
Talla

Wata Kungiyar Kare Hakin Bil-adama a yankin ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun bude wuta ne kan ayarin motocin da ke dauke da Kwaminshinan a yammacin jiya Alhamis, abin da kuma ya jikkata wasu daga cikin jami'an da ke tare da shi da suka hada da Kantoman Lebialem, Zacharie Ungithoh da  ya samu mummunan rauni.

Tawagar Kwamishinan na kan hanyarta ne na zuwa ganin gidan wani Minista da 'yan awaren suka kona.

Al’amuran tsaro dai na kara tabarbarewa a  'yan kwanakin nan a yankuna biyu da ke amfani da Turancin Ingilishi a Kamaru.

Ko a ranar Talatar da ta gabata, ‘yan bindigar sun hallaka wani dan Tunisiya guda da suke garkuwa da shi lokacin da jami’an tsaro suka yi kokarin kubutar da mutane hudu da ke hannunsu da suka hada da ‘yan Tunisiya 2 da kuma ‘yan Kamaru 2.

A farkon wannan shekar, ‘yan awaren sun yi garkuwa da wani Kantomar yankin da kuma Kwamishinan Kula da walwalar al'umma, wanda har yanzu babu labarinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.