Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta saki wasu yan matan Dapchi

A yau talata,kungiyar Boko Haram ta saki wasu  daliban makatarantar Dapchi,a baya dai gwamnatin Najeriya ta zabi ci gaba da tattaunawa a maimakon amfani da karfi domin kubutar da daliban Dapchi da sauran daliban Chibok da ke hannun Boko Haram.

Daliban Dapchi da kungiyar Boko Haram ta saki
Daliban Dapchi da kungiyar Boko Haram ta saki rfi hausa
Talla

Rahotanni daga yankin na nuni da cewa biyar daga cikin daliban sun mutu a lokacin da yan boko haram ke kokarin ficewa da su daga Dapchi.

Indan aka yi tuni Shugaba Buhari ya ce, Najeriya na aiki cikin wata yarjejeniya da kungiyoyin kasashen ketare da masu sulhu don ganin an ceto ‘yan matan ba tare da cutar da su ba.

Shugaban ya kuma mika godiya ga Amurka bisa tallafinta na yaki da ta’addanci a Najeriya, yayin da kuma ya jinjina wa dakarun kasar da ya ce, suna bukatar karin samun horo da kayayyakin aiki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.