Isa ga babban shafi
Mali

Canada za ta aike da jiragen yaki Mali

Canada za ta aike da dakarun soji hade da jiragen yaki baya ga kayakin agajin magunguna zuwa kasar Mali don taimakawa rundunar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta ta Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a kasar mai fama da hare-hare ta’addanci.

Canada ta ce jiragen yakin, za su share tsawon watanni 12 a kasar ta Mali mai fama da ayyukan ta’addanci kamar dai yadda ministar wajen kasar Chrystia Freeland ta sanar a wannan litinin.
Canada ta ce jiragen yakin, za su share tsawon watanni 12 a kasar ta Mali mai fama da ayyukan ta’addanci kamar dai yadda ministar wajen kasar Chrystia Freeland ta sanar a wannan litinin. REUTERS/Ahmad Nadeem
Talla

Canada ta ce jiragen yakin, za su share tsawon watanni 12 a kasar ta Mali mai fama da ayyukan ta’addanci kamar dai yadda ministar wajen kasar Chrystia Freeland ta sanar a wannan litinin.

Chrystia Freeland ta ce matakin tabbatarwa ce kan alkawarin da shugaba Justin Trudeau ya dauka a shekarar 2016 na aikewa da dakaru 600 kasar ta Mali.

Fiye da jami’an wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya 80 ne suka mutu a Mali daga shekarar 2013 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.