Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Yan adawa a kasar Cote d'Ivoire za su yi zanga zangar lumana kan hukumar zabe

adawa a kasar Cote d’Ivoire sun kirayi magoya bayansu da su fito tattakin lumana a ranar 22 ga wannan wata na maris domin nuna bacin ransu.A lokacin taron gangamin magoya baya da aka gudanar a ranar assabar ne, Shugaban gungun jam’iyun adawar kasar, Ensemble pour la démocratie et la souveraineté (EDS), Armand Ouegnin, ya yi kiran gudanar zanga zangar lumanar domin bayyana bacin ransu da hukumar zaben kasar CEI da ‘yan adawar ke zargi da karkata a bangaren gwamnati

shugaban kasar cote d'ivoir Alassane Ouattara,
shugaban kasar cote d'ivoir Alassane Ouattara, SIA KAMBOU / AFP
Talla

Za a gudanar da zaben yan majalisar dattawan kasar ne a ranar 24 ga wannan wata na maris, kafin a gudanar da na kananan hukumomi duk a cikin wannan shekara ta 2018 s a wani wa’adi nan gaba da ba a kayyade,

Sai dai zaben shugabancin kasar da za a gudanar a 2020 shine ya fi daukar hankali a kasar mai arizikin Koko a yammacin Afrika dake ta kokarin ganin ta magance matsalolin siyasa da kuma na soja da ke addabarta

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.