Isa ga babban shafi
Angola

Dos Santos na Angola ya karawa kansa wa'adin shekara guda

Jagoran jam’iyyar MPLA mai mulki a Angola kuma tsohon shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos ya ce ba zai ajje shugabancin jam’iyyar a bana kamar yadda ya alkawarta a baya ba, a don haka dole ne jam’iyyar ta jira har zuwa watan Disamba ko Afrilun shekara mai zuwa kafin zaben wanda zai maye gurbinsa.

Wani zaman majalisar gudanarwar kasar ta Angola karkashin jagorancin jam'iyyar MPLA mai mulkin kasar.
Wani zaman majalisar gudanarwar kasar ta Angola karkashin jagorancin jam'iyyar MPLA mai mulkin kasar. RFI/Daniel Frederico
Talla

Kafin yanzu dai Eduard dos Santos ya alkawarta barin dukkanin harkokin siyasa a shekarar da muke ciki ta 2018.

A bara ne dai shugaba Dos Santos ya zabi Joao Lourenco ya maye gurbinsa na shugabancin kasar bayan da ya cika shekaru 38 a karagar mulki yayinda ya nada kansa a matsayin shugaban jam’iyyar ta MPLA mai mulki, matakin da ya raba ikon shugabancin kasar zuwa bangare biyu.

Shugaba Dos Santos dai duk da kasancewar ba shi ne shugaban kasar ba, amma kusan shi ke jan ragama tare da tsara duk abin da zai wakana abin da ke nuna cewa dai har yanzu shi ke juya kasar tun bayan karbar mulki daga Portugal a 1975.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.