Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty na zargin kamfanonin mai da gurbata muhalli a Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kaddamar da bincike kan yadda kamfanonin mai na Shell na ENI ke gurbata muhalli sakamakon tsiyayar mai a yankin Niger Delta.

Tambari Shell da Eni a Najeriya
Tambari Shell da Eni a Najeriya www.rfi.fr
Talla

Kungiyar ta yi zargin cewa kamfanonin sun haddasa tsiyaya wurare akalla 89 sakamakon fashewar bututun mai lamarin da ya yi sanadiyyar gurbata muhalli a yankin na Niger Delta.

Rahoon Amnesty ya ce bututun mai 46 mallakin Shell ne suka zubar da gurbataccen mai yayin da kamfanin ENI ya haddasa irin wannan tsiyaya har sau 43.

Alkaluman da kungiyoyi masu zaman kansu suka tattara a shekara ta 2011, na tabbatar da cewa an samu tsiyarar mai sau 1.010 daga Shell wanda ya haura ganga dubu 110, yayin da kamfanin ENI ya samu irin wannan tsiyaya har sau 820 mai nauyin ganga dubu 26 da 286 a bayanan da kungiyoyin suka tattara a shekarar 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.