Isa ga babban shafi
Guinea

Zazzafar zanga-zanga ta barke a Guinea Conakry

Dubban matasa sun rufe hanyoyi yayinda wasu ke ci gaba da kona tayoyi a manyan titunan babban birnin kasar ta Guniea Conakry bayan kammala zaben cikin gida. Zanga-zangar adawa da zaben na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar malaman kasar ke ci gaba da yajin aiki hade da zanga-zanga kan matakin ilimi a kasar.

Galibin masu zanga-zangar da suka kunshi mata da kananan yara sun yi dafifi a kofar fadar gwamnatin kasar tare da neman lallai shugaba Alpha Conde ya dauki matakin da ya kamata don dai daituwar al'amura a kasar.
Galibin masu zanga-zangar da suka kunshi mata da kananan yara sun yi dafifi a kofar fadar gwamnatin kasar tare da neman lallai shugaba Alpha Conde ya dauki matakin da ya kamata don dai daituwar al'amura a kasar. Carol Valade / RFI
Talla

An faro zanga-zangar ne tun bayan fitowar sakamakon zaben ranar 4 ga watan Fabarairun da ya gabata wanda ya nuna jam'iyyar Shugaba Conde ce ke da gagarumin rinjaye.

Zaben cikin gidan dai shi ne irinsa na farko tun bayan shekarar 2005 da ya gudana a kasar wanda kuma bangarorin adawa suka yi fatan samun sauyi.

Kawo yanzu dai akalla masu zanga-zanga 12 aka hallaka yayinda jami'an tsaro suka kame da dama.

A bangare guda kuma tun daga ranar 12 ga watan Fabarairun da ya gabata kungiyar malaman makarantar ke yajin aiki hade da zanga-zanga ba kuma tare da gwamnati ta dauki mataki ba.

Galibin masu zanga-zangar da suka kunshi mata da kananan yara sun yi dafifi a kofar fadar gwamnatin kasar tare da neman lallai shugaba Alpha Conde ya dauki matakin da ya kamata don dai daituwar al'amura a kasar.

Ko a ranar mata ta duniya da ta gudana a makon jiya ma, daruruwan mata sun fito sanye da fararen kaya tare da yin dafifi a farfajiyar fadar shugaban kasar don neman hakkinsu tare da dai dai to a gwamnatinsa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.