Isa ga babban shafi
Sierra-leone

Akwai yiwuwar zaben Saliyo ya kai ga zagaye na 2

Akwai yiwuwar sai an kai ga kada kuri’a zagaye na biyu a zaben shugabancin kasar Saliyo, idan aka yi la’akari da yadda ake tafiya kan kan kan tsakanin manyan ‘yan takarar shugabancin kasar 2, yayinda a ranar Asabar aka kammala kidayar rabin kuri’un da aka kada.

Julius Maada Bio, dan takarar shugabancin kasar Saliyo, a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta SLPP, dauke da 'yarsa yayin kada kuri'a a birnin Freetown, na Saliyo.
Julius Maada Bio, dan takarar shugabancin kasar Saliyo, a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta SLPP, dauke da 'yarsa yayin kada kuri'a a birnin Freetown, na Saliyo. REUTERS/Olivia Acland
Talla

Sakamakon kidayar rabin kuri’un ya nuna cewa, tsohon ministan harkokin wajen kasar kuma dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC Samura Kamara da kuma dan takarar jam’iyyar adawa ta SLPP Julius Maada Bio, kowannensu ya samu kashi 43.

Sauran ‘yan takarar da ke biye da su wato Kandeh Yumkella da Samuel Sam-Sumana, na da kashi 6.7 da kuma 3.4 na rabin kur’un da aka kidaya.

Akwai sauran ‘yan takara 12 da ke neman maye gurbin shugaban kasar ta Saliyo mai ci Ernest Bai Koroma, bayan kammala wa’adin shugabancinsa guda biyu na shekaru biyar kowanne.

Daga cikin kalubalen da ke gaban sabon shugaban kasar ta Saliyo da za’a zaba akwai kyautata tsarin kula da lafiya na kasar, baya shawo kan cutar Ebola da ta hallaka akalla mutane 4000, kuma zuwa yanzu kimanin manyan likitoci 200 ne ke lura mutanen kasar da yawansu ya kai miliyan 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.