Isa ga babban shafi
Sierra-leone

Al'ummar Saliyo na gudanar da zaben shugaban kasa

A yau Laraba al’ummar kasar Sierra Leone ke kada kuri’a domin zaben wanda zai maye gurbin shugaba Ernest Bai Koroma wanda ya share tsawon shekaru 10 yana mulkin kasar.

Sama da mutane miliyan 3 ne ke kada kuri'a a zaben Saliyo da ke gudana a yau
Sama da mutane miliyan 3 ne ke kada kuri'a a zaben Saliyo da ke gudana a yau Reuters/Joe Penney
Talla

Sama da mutane milyan 3 ne suka yi rajista domin kada kuri’a a zaben, in da ‘yan takara 16 za su fafata da juna a wannan karamar kasa da ke yammacin Afrika.

Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka fi daukar hankulan jama’a a zaben sun hada da Samura Kamara, wanda ya fito daga jam’iyya mai mulki wato APC, sai kuma babban mai hamayya da shi wato Kandeh Yumkella, wanda tsohon mataimakin babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Julius Maada Bio, wanda ya mulki kasar kafin juyin mulki a 1996.

Batun yaki da talauci da kuma samar wa matasa ayyukan yi, su ne suka mamaye yakin neman zaben, lura da cewa a daidai lokacin da Saliyo ke farfadowa daga matsalolin yakin basarar tsawon shekaru, sai kasar ta sake cin karo da wani ibtila'in  cutar Ebola.

Ko baya ga zaben shugaban kasa, a hannu daya jama’a za su kada kuri’unsu domin sabunta Majalisar Dokoki duk a yau Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.