Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Kisan da aka yi wa wani karamin yaro mai shekaru 4 aduniya ya girgiza birnin Abijan.

# Ni ne Buba itace Kalmar da ta mamaye shafukan sada zummunta a yan kwanakin nan a kasar Cote d’Ivoire.

Masu zanga zangar nuna bacin ran kisan Buba
Masu zanga zangar nuna bacin ran kisan Buba http://atoo.ci
Talla

Buba, sunan wani karamin yaro ne mai shekaru 4 a duniya da aka yiwa kisan gilla a birnin Abijan, domin kawai biyan bukatar samun abin duniya duniya bisa umarnin Matsafa.

Al’amari irin wannan ba sabon abu bane a kasar ta Cote d’Ivoire, sai dai a wanan karo abin ya haifar da mummunan bacin rai ga al’umma, har zuwa mataki na koli na mulkin kasar.

Za a iya cewa dai, hoton wannan yaro shi ne hoton da aka fi gani ko sani a kasar.

karamin yaro ne cikin raha ya daga yatsunsa na hannun dama manunin da babba dake nuna alamar nasara. (V)

Buba wanda cikaken sunansa Abubakar Sidiq Traore, ya bata ne a makon ranar 24 ga watan janairun da ya gabata, a anguwar Williamsville dake tsakkiyar birnin, an kuma gano gawar sa ne a Cocody-Angré, dake gabashin Abijan, hannuwansa da kafafunsa a daure an yi masa yankan Rago.

Dubun wani matashi mai kera ‘yan kunne dan shekaru 27 a duniya Etienne Sagno ta cika, ya nuna wa ‘yan sanda inda gawar Buba take.

A wata firarar neman bahasi da yan sanda suka nada a hoton bidiyo da dare a wurin da aka gano gawar, matashin ya tabbatar da cewa, shi ya aikata kisan, kuma ya bada bahasi dalla dalla yadda ya gudanar da wannan kazamin aiki.

Kuma manufarsa ta yin haka shine kwadayin samun abin duniya, wanda ke kaiwa ga kashe rai na dan adam.

Wannan matashi dai ya sanar da yan sanda cewa ya yi haka ne bisa bin umarnin wani Boka wanda yace masa idan ya yanka mutum bukatarsa zata fi saurin biya.

Ta bakin hukumar yan sanda an share tsawon shekaru ba a kawo masu rin wannan mummunan lamari na kisa da sunan tsafi wajen neman tara abin duniya ba.

sai dai kuma a yan makwannin nan ana samun bayanan dake cewa yara suna bacewa a birnin na Abijan.

Mutuwar Buba ta haifar da bacin rai mai yawa a kasar ta Cote d’Ivoire. Gwamnati har zuwa ga mai dakin shugaban kasa Dominique Ouattara sun bayyana jimaminsu kan kisan Buba ta shafukan sada zumunta

A ranar assabar da ta gabata wasu gungun mutane sun yi tattaki jerin gwanon cikin lumana a Cocody-Angré suna rera take dake cewa kar a sake maimaita wannan ! »

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.