Isa ga babban shafi

Kungiyar JNIM ta yi ikirarin kai hare-haren birnin Ouagadugou

Wata kungiya da ke kiran kanta da Jama’a Nusratul-Islam ta yi ikirarin ita ce ta kai tagwayen hare-hare kan ofishin jakadancin Faransa, da kuma hedikwatar sojojin kasar Burkina Faso a birnin Ouagadugou.

Shingen jami'an tsaron da aka kafa akan titin da yake kai wa ga hedikwatar sojojin Burkina Faso a birnin Ouagadugou, bayan tagwayen hare-haren da aka kai wa sojin da kuma ofishin jakadancin Faransa.
Shingen jami'an tsaron da aka kafa akan titin da yake kai wa ga hedikwatar sojojin Burkina Faso a birnin Ouagadugou, bayan tagwayen hare-haren da aka kai wa sojin da kuma ofishin jakadancin Faransa. Reuters
Talla

Kungiyar wadda ta yi wa Al Qaeda mubaya’a ta kara da daukar alhakin hare-haren da ake kai wa baya bayannan kan fararen hula da jami’an tsaro a yankunan Afrika ta Yamma, wadanda ta ce martani ne kan hallaka daya daga cikin jagororin kungiyar Muhd Hassanal-Ansari, a wani samame da sojin Faransa suka kai.

Akalla mutane 28 ne suka hallaka yayin da wasu 80 suka jikkata sakamakon hare-haren na birnin Ouagadugu.

Ministan tsaron Burkina Faso, Clement Sawadogo, ya ce an kai wa Hedikwatar sojin kasar harin kunar bakin waken ne da mota makare da bama-bamai, inda sojoji da wasu fararen hula da dama suka hallaka.

Burkina Faso tana daga cikin kasashe 5 da suka hada da Nijar, Muritania, Chadi da Mali, karkashin kungiyar G5 Sahel da suka kafa rundunar sojin hadin gwiwa da zata yaki ta’addanci a yankin Sahel da ke fuskantar Karin barazanar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.