Isa ga babban shafi

An shawo kan harin 'yan ta'adda a Ouagadugou - Faransa

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da shawo kan duk wata barazanar tsaro da ke akwai a babban birnin kasar Burkina Faso, Ouagadogou, bayan hare-haren da aka kai wa ofishin jakadancinta da kuma Hedikwatar rundunar sojin Burkina Faso.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian. REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Ministan harkokin waje na Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce ba’a samu hasarar dan kasar oda daya ba inda ya tabbata da hallaka baki daya maharan 4.

Tagwayen hare-haren da aka kai kan Ofishin Jakadancin Faransa da kuma Hedikwatar sojojin Burkina Faso, a babban birnin kasar Ouagadogou, jiya Juma’a sun hallaka mutane 28 tare da raunata wasu 80.

Ministan tsaron Burkina Faso, Clement Sawadogo, ya ce an kai wa Hedikwatar sojin kasar harin kunar bakin waken ne da mota makare da bama-bamai, inda sojoji da wasu fararen hula da dama suka hallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.