Isa ga babban shafi
DRC

MDD ta damu matuka da rikicin Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta da mutuwar mutane biyu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a Jamhuriyar Demokradiyar Congo. Majalisar ta bukaci taka tsan-tsan kan matakan da jami’an tsaro ke dauka.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun yi aranga da jami'an tsaron Congo, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun yi aranga da jami'an tsaron Congo, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Sanarwar da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da aikin samar da zaman lafiya ya bayar a Kinshasa ta bayyana damuwarsa da kashe mutanen biyu a Mbandaka da Kinshasa duk da umurnin da aka bai wa jami’an tsaro na kauce wa amfani da karfin da ya wuce kima.

Leila Zerrougui, jakadiyar Majalisar a Kinshasa ta ce, jami’ansu da ke sa ido kan halin da ake ciki, sun gano cewa an jikkata mutane 47, yayin da aka kama sama da 100.

Majalisar ta bukaci hukumomin kasar Congo da su yi taka tsan-tsan wajen kai hari kan fararen hular da kuma gudanar da bincike kan abin da ya faru.

Sanarwar ta kuma bukaci bangarorin siyasar Congo da su hada kansu wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2016, wanda shi ne kadai hanyar gudanar da zabe mai inganci da kuma mika mulki domin inganta demokiradiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.