Somalia
Harin bam ya hallaka mutane 27 a Mogadishu
Harin wasu bama-bamai da aka dana a jikin motoci ya hallaka akalla mutane 27 tare da jikkata wasu 20 a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia.
Wallafawa ranar:
Talla
Harin wanda budewar wuta ya biyo bayansa, ya auku ne a gaf da fadar gwamnatin kasar ta Somalia.
Harin da kungiyar al-Shebaab ta dauki alhakin kai wa ya zo ne kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta yi gargadin yiwuwar aukuwar harin ta’addanci a babban birnin kasar.
A watan Oktoban bara, wani harin bam da aka dana a babbar mota, ya hallaka mutane 512, wanda shi ne hari mafi muni da aka taba gani a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu