Isa ga babban shafi
France-Sahel

Taron taimaka wa rundunar tsaron kasashen yankin Sahel a Brussels

Yau juma’a, ana gudanar da taro da nufin tara kudaden tallafi ga rundunar G5-Sahel, taron da ke gudana a birnin Bruxelles na kasar Belgium.

Tambarin rundunar G5-Sahel
Tambarin rundunar G5-Sahel © RFI/Olivier Fourt
Talla

Ko baya ga shugabannin kasashe 5 mambobi a wannan runduna, da suka hada da Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da kuma Nijar, akwai shugabannin kasashe da suka hada da Faransa da kuma Jamus da ke halartar taron nay au.

Har ila yau karon farko kasashen Turkiyya da Afirka ta Kudu za su halarci zaman, tare da yiyuwar bayar da tasu gudunmuwa domin daukar nauyin wannan runduna ta G5-Sahel.

Rundunar dai na bukatar Euro milyan 423 domin tafiyar da ayyukanta da suka shafi tabbatar da tsaro da kuma fada da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.