Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 224 suna fama da yunwa a Afrika - MDD

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewar Afirka na fuskantar bala’in yunwa ganin yadda yanzu haka mutane miliyan 224 ke fama da karancin abinci mai gina jiki a nahiyar, sakamakon sauyin yanayi da kuma tashe tashen hankula.

Wasu kananan yara 'yan gudun hijira a sansanin Al-cadaala da ke birnin Mogadishu na kasar Somalia.
Wasu kananan yara 'yan gudun hijira a sansanin Al-cadaala da ke birnin Mogadishu na kasar Somalia. REUTERS/Feisal Omar
Talla

Daraktan hukumar samar da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya dake kula da Afirka Bukar Tijani, ya bayyana cewar halin da ake ciki yanzu haka, sakamakon abin fargaba ne, musamman ganin yadda ake saran adadin mutanen da ke Afirka zai kai biliyan 1 da miliyan 700 nan da shekara ta 2030.

Jami’in yace rahsin abinci mai gina jiki ya karu daga kashi 21 a shekarar 2015 zuwa kashi 23 a shekarar 2016, yayin da adadin mutane dake fama da yunwa ya karu daga miliyan 200 zuwa miliyan 224.

Tijani ya bayyana sauyin yanayi da ambaliya da fari da kuma rashin ingancin abincin da ake nomawa a matsayin wasu daga cikin matsalolin dake haifar da yunwa.

Daraktan ya kuma bayana tashe tashen hankula a kasashen Somalia, Sudan ta kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a matsayin abubuwan da suka sanya matsalar yin kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.