Ana zargin Moses Thomas da bada umarnin kisan gillar ne a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 1990, yayin da yake rike da mukamin Kanal a rundunar sojin Liberia, wanda ya tsere zuwa Amurka bayan karewar yakin basasar kasar.
Tuni dai Thomas ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa na take hakkin dan adam.
Kisan gillar da aka yi ma masu ibada a Mujami’a da ke Monrovia, daya ne daga cikin mafi munin laifukan yaki da aka tafka a yakin basasar Liberia da ya shafe shekaru 14, kafin kawo karshensa a shekarar 2003.