Masar
Kotun Masar ta daure 'yan uwa Musulmi saboda bore
Wata Kotu a Masar ta yanke wa ‘yan kungiyar ‘yan uwa Musulmi 33 hukuncin dauri daga shekaru 7 zuwa rai-da-rai saboda tashin hankalin da aka yi a lokacin wata zanga zanga a shekarar 2014.
Wallafawa ranar:
Talla
Tashin hankalin ya biyo bayan juyin mulkin da soji suka yi wa shugaba Mohammed Morsi, bayan zanga zangar adawa da gwamnatinsa.
Bayanan kotun sun nuna cewar, an yanke wa mutane 17 hukuncin rai da rai, yayin da 16 kuma suka samu hukuncin da bai kai haka ba.
Daurin rai-da-rai a kasar Masar na dauke da hukuncin shekaru 25 ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu