'Yan Sudan ta Kudu sun yi wa Amurka bore
Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Amurka da na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Juba domin bayyana bacin ransu kan matakin haramta wa Sudan ta Kudu sayen makamai.
Wallafawa ranar:
Masu zanga-zangar sun mika takardar korafinsu ga jami’an Majalisar Dinkin Duniyar, yayin da wasu kuma suka kai musu hari, in da aka raunana wata 'yar jarida mai daukar hoto.
Kasar Amurka ta gabatar da kudirin hana sayar wa Sudan ta kudu makamai saboda yadda bangarorin da ke rikici a kasar suka gaza aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla.
Rikicin basasar kasar ya haddasa asarar rayukan dubban mutane, yayin da miliyoyi suka kaurace wa gidajensu, in da kuma wasu da dama suka tsindima cikin matsalar yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu