Jami’an gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo na fuskantar takunkumai daga Amurka
Amurka ta sanar da takunkumai a kan wasu manyan jami’an gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sakamakon rawar da suke takawa a rikicin siyasar kasar.
Wallafawa ranar:
Kafin nan, Faransa ta jima da sanya wa mutanen hudu takunkumai tare da kwace kadarorinsu a kasar.
Tun a baya gamayyar jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Congo suka cimma matsaya, domin tilastawa shugaban kasar Joseph Kabila, sauka daga mukaminsa.
Yan adawar sun tattauna ne kan zaman dirshan da Kabila ke cigaba da yi a kujerar shugabancin kasar tun daga shekarar 2001.
Yan adawan sun bayyana cewa zaman kabila a kujerar shugabancin kasar ya haifar da koma bayan gaske a fanoni daban –daban,saukar sa ne mafuta ga wannan kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu