Isa ga babban shafi
Sahel

Shugabannin yankin Sahel 5 na taro kan rundunar G5

Shugabannin kasashen da suka kafa Rundunar G5 Sahel domin yaki da Yan ta’adda sun gudanar da wani taro da ministan tsaron Faransa domin tattauna yadda za’a samo kudaden tafiyar da rundunar wanda tuni ta fara aiki.

Ana saran Rundunar ta fara aiki gadan-gadan a tsakiyar shekarar nan bayan kammala samo kudaden da za a tafiyar da ita.
Ana saran Rundunar ta fara aiki gadan-gadan a tsakiyar shekarar nan bayan kammala samo kudaden da za a tafiyar da ita. CHRISTOPHE ARCHAMBAULT / AFP
Talla

Shugabannin kasashen 5 da suka hadar da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Jamhuriyar Nijar sun gana da Florence Parly, ministan tsaron Faransa yau a birnin Yamai inda kasar ta ce ta fara bayyana goyan bayan kafa rundunar.

Kasashen biyar tare da Najeriya da Kamaru na fama da matsalar ayyukan Yan ta’adda wadanda suka hallaka dubban mutane.

Ana saran rundunar da kungiyar ta kafa mai dakaru 5,000 ta shiga aiki gadan gadan a tsakiyar wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.