Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bukaci Tunibu ya sasanta 'ya'yan jam'iyyar APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada tsohon Gwamnan Jihar Lagos Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wani kwamiti na musamman wanda zai sasanta ‘yayan Jam’iyyar APC da kuma hada kan su kafin zaben shekara mai zuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu bayan kammala wani taro kan jam'iyyar APC a fadar shugaban ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu bayan kammala wani taro kan jam'iyyar APC a fadar shugaban ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar. NAN
Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta nuna cewar kwamitin na Tinubu zai mayar da hankali wajen sasanta rigingimun da aka samu tsakanin yayan jam’iyar APC da shugabannin ta da kuma masu rike da mukaman gwamnati.

Rahotanni daga sassan Najeriya na nuna rikice rikice da ake samu a Jam’iyyar mai mulki da kuma korafe korafe wajen raba mukaman gwamnati baya ga zargin watsi da asalin wadanda suka goyawa Buhari baya a zaben shekarar 2015 na ci gaba da girmama.

Jam'iyyar ta APC wadda ta hadaka ce tsakanin jam'iyyun kasar uku da suka dunkule yayin kakar zabe ta 2015 don hambarar da gwamnatin Goodluck Jonathan karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, masharhanta kan al'amuran siyasa na ganin za ta iya gamuwa da gagarumin tsaiko matukar bata hada kan 'ya'yan tare da sulhunta rikice-rikicen da ke tsakaninsu ba, gabanin babban zaben kasar a badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.