Isa ga babban shafi
Kenya

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Kenya

Jami'an 'yan sanda a kasar Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga zangar neman ganin an bude tashoshin talabijin din kasar da aka rufe saboda haska bikin rantsar da Jagoran adawar kasar Raila Odinga a matsayin shugaban al'umma.

Wani shaidar gani da ido ya ce Yan Sandan sun tarwatsa dandazon masu zanga zangar ne lokacin da suke tattaki zuwa ofishin gwamnatin a Nairobi babban birnin kasar, dangane da kin bude gidajen talabijin din.
Wani shaidar gani da ido ya ce Yan Sandan sun tarwatsa dandazon masu zanga zangar ne lokacin da suke tattaki zuwa ofishin gwamnatin a Nairobi babban birnin kasar, dangane da kin bude gidajen talabijin din. citizentvkenya
Talla

Wani shaidar gani da ido ya ce Yan Sandan sun tarwatsa dandazon masu zanga zangar ne lokacin da suke tattaki zuwa ofishin gwamnatin a Nairobi babban birnin kasar, dangane da kin bude gidajen talabijin din.

Tuni dai matakin gwamnatin Kenyan ya fara fuskantar suka daga manyan kasashen Duniya irin su Birtaniya Amurka dama Majalisar Dinkin Duniya.

A makon jiya ne Gwamnatin Kenya ta bijirewa umurnin kotu kan bude wasu manyan gidajen talabijin 3 da suka kunshi Citizen TV, KTN da kuma NTV wadanda ta kulle tun bayan da suka haska bikin rantsar da Raila Odinga kai tsaye.

Kotun dai ta bukaci bude gidajen talabijin kafin ci gaba da sauraron karar da kafofin suka shigar gabanta.

A bangare guda kuma wasu masu fafutukar kare hakkin dan adam sun shigar da makamanciyar karar gaban kotu inda suka bukaci kame wasu ministocin Uhuru Kenyatta biyu hade da wasu manyan jami'an gwamnatinsa.

A cewar Okiya Omtatah, guda cikin masu fafutukar ba zai yiwu su zuba ido su ci gaba da kallon take hakkin da gwamnatin kasar ke yi ba, bugu da kari kuma ga rashin mutunta umarnin kotu.

Kawo yanzu dai babu wani martini daga bangaren gwamnatin kasar dangane da tarwatsa masu zanga-zangar ko kuma kan batun sabon sammacin kotun da za su fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.