Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Ba zan yi murabus ba- Jacob Zuma

Duk da ganawar da wasu manyan jam’iyyar ANC suka yi da shi domin ganin cewa ya yi marabus daga mukaminsa a cikin daren jiya, shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce bazai sauka ba, a maimakon haka ma ya tsara gabatar wa al’ummar kasar da wani jawabi ne a cikin kwanaki uku masu zuwa.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na cikin tsaka-mai-wuya
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na cikin tsaka-mai-wuya REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A cikin daren jiya lahadi, manyan jami’an jam’iyyar ta ANC 6 ne suka gana da Zuma a fadarsa da ke Pretoria, in da suka yi kokarin shawo kansa da ya yi marabus lura da sabuwar barazanar da yake fuskanta ta tsigewa daga masu hamayya da shi.

Kafin wannan ganawa dai tuni kwamitin kolin jam’iyyar ya tsara gudanar da wani taron gaggawa a wannan Litinini domin duba matakan da suka dace a dauka sakamakon yadda adadin masu bukatar shugaban ya sauke ke dada karuwa daga lokacin da aka zabi mataimakinsa Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban ANC cikin watan disambar da ya gabata.

Duk da cewa Ramaphosa bai bayyana shawarsa ta maye gurbin Zuma a matsayin shugaban kasa ba, to amma wanda ke rike da matsayi na uku mafi girma a jam’iyyar Gwede Mantashe ya fito fili karara domin zawarcin wannan matsayi lura da yadda kwarjinin shugaban ke ci gaba da raguwa a tsakanin ‘yayan jam’iyyar.

A wannan Litinin bangarori 3 da suka kunshi masu adawa da kuma magoya bayan shugaban ne suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga a birnin Johannesburg, yayin da ‘yan adawa a Majalisa suka bukaci wani ya gabatar da jawabin shekara-shekara na shugaban kasar amma ba Jacob Zuma ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.