Isa ga babban shafi

Shugaban Equatorial Guinea ya rushe gwamnatin da ya kafa

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, ya rushe majalisar zartarwar gwamnatinsa, ciki harda mukamin Firaministan kasar da kuma baki dayan mataimakansa guda 3.

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.
Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Nan da kwanaki masu zuwa ne ake sa ran shugaban zai sanar da kafa sabuwar gwamnati.

Obiang ya kafa gwamnatin da ya rushe mukamanta ne, a watan Yunin shekarar 2016, bayan lashen zaben shugabancin kasar da ya yi a watan Afrilun shekarar ta 2016 da kashi 93.7 na kuri’un da aka kada.

A watan Nuwamban da ya gabata kuma aka yi zaben ‘yan majalisun kasar da na kananan hukumomi, wanda shi ma jam’iyya mai mulki ta lashe kujerun majalisar kasar 99 daga cikin 100.

Shugaba Theodoro Obiang wanda ya ke mulkin Equatorial Guinea tun daga shekarar 1979, yana fsukantar suka bisa zargin dankwafe ‘yan adawa, tafka magudin zabe da kuma cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.