Isa ga babban shafi
Afrika

An ceto ma'aikatan hako zinare 950 a Afrika ta kudu

A Afrika ta Kudu  a yau juma'a an ceto ma’aikatan hako zinare 950 da suka makale cikin karkashin kasa tun a jiya Alhamis.Kamfanin da mai’akatan ke wa aiki, mai suna Sibanye-Stillwater, ya ce kakkarfar guguwa ce ta haddasa katsewar lantarki a filin hakar ma’adanan da ke kauyen Theunissen da ke gaf da birnin Welkom.

Filin hakar ma’adanan da ke kauyen Theunissen da ke gaf da birnin Welkom a Afrika ta Kudu
Filin hakar ma’adanan da ke kauyen Theunissen da ke gaf da birnin Welkom a Afrika ta Kudu (Carte : M. Gilles-Garcia / RFI)
Talla

Mai Magana da yawun kamfanin hakar ma’adanan, James Wellsted ya tabbatar da cewa ma’aikatan su 955 da ke makale cikin karkashin kasar, sun samu kulawa da ta dace, .

Wellsted ya ce kwararru sun taimaka wajen gyara matsalar lantarkin tareda samar da hanyar ceto ma’aikatan, wadanda tun a jiya aka samu nasarar zakulo 272.

Zurfin ramin hako zinaren da ma’aikatan suke ciki mai dauke da matakai 23, ya kai mitoci dubu daya (1,000).

Daruruwan iyalan ma’aikatan sun yi dafifi zuwa filin hakar ma’adanan cikin damuwa .

Lamarin ya sanya kungiyoyin ma’aikatan hakar ma’adanai a Afrika ta Kudu, yin kira ga ilahirin mambobinsu da su kauracewa aiki a karkashin yanayi mai hadari da gangan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.