Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/07 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/07 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/07 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/07 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/07 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/07 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 22/07 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 21/07 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 22/07 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 21/07 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 22/07 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

An ceto ma'aikatan hako zinare 950 a Afrika ta kudu

media Le drame s'est produit dans une mine de la ville de Welkom, à 250 kilomètres … Filin hakar ma’adanan da ke kauyen Theunissen da ke gaf da birnin Welkom a Afrika ta Kudu (Carte : M. Gilles-Garcia / RFI)

A Afrika ta Kudu  a yau juma'a an ceto ma’aikatan hako zinare 950 da suka makale cikin karkashin kasa tun a jiya Alhamis.

Kamfanin da mai’akatan ke wa aiki, mai suna Sibanye-Stillwater, ya ce kakkarfar guguwa ce ta haddasa katsewar lantarki a filin hakar ma’adanan da ke kauyen Theunissen da ke gaf da birnin Welkom.

Mai Magana da yawun kamfanin hakar ma’adanan, James Wellsted ya tabbatar da cewa ma’aikatan su 955 da ke makale cikin karkashin kasar, sun samu kulawa da ta dace, .

Wellsted ya ce kwararru sun taimaka wajen gyara matsalar lantarkin tareda samar da hanyar ceto ma’aikatan, wadanda tun a jiya aka samu nasarar zakulo 272.

Zurfin ramin hako zinaren da ma’aikatan suke ciki mai dauke da matakai 23, ya kai mitoci dubu daya (1,000).

Daruruwan iyalan ma’aikatan sun yi dafifi zuwa filin hakar ma’adanan cikin damuwa .

Lamarin ya sanya kungiyoyin ma’aikatan hakar ma’adanai a Afrika ta Kudu, yin kira ga ilahirin mambobinsu da su kauracewa aiki a karkashin yanayi mai hadari da gangan.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure