Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zimbabwe zata maida wa fararen fata izinin mallakar gonaki

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta ce zata baiwa manoma fararen fata izinin mallakar filayen noma na shekaru 99, kamar yadda ake baiwa takwarorin su bakaken fata.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa.
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Matakin yana daga cikin sauyin da aka samu a karkashin shugabancin Emmerson Mnangagwa, wanda ya sha alwashin magance matsalar da aka samu tsakanin tsohuwar gwamnati Robert Mugabe da manoman fararen fata.

Sanarwar da ma’aikatar kula da ayyukan noma ta Zimbabawe ta fitar, ta ce daga yanzu za’a baiwa daukacin manoman da suka rage a kasar izinin ci gaba da aiki a filayen su na tsawon shekaru 99.

Har yanzu dai akwai ragowar manoma fararen fata akalla 400 a Zimbabwe, bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, ya kori fararen fatar manoma sama da dubu hudu daga kasar, tare da mika gonakinsu ga ‘yan kasa.

A lokacin da turawan mulkin mallaka ke iko da Rhodesia kafin daga bisani an canza sunan zuwa Zimbabwe, mafi akasari sun kwace manyan gonakin bakaken fata ‘yan kasar, kuma har zuwa lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1980, gonakin sun ci gaba da zama a hannun turawan.

Sai dai bayan shekaru 20, shugaba Robert Mugabe, ya bada umarnin kwace gonakin daga karkashin turawan, domin mika su ga ‘yan kasa, saboda gyara zaluncin da aka tafka a zamanin mulkin mallaka, kamar yadda ya fada a waccan lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.